Barazanar cocin Anglika na Najeriya ga Ingila

A Najeriya, Bishop-bishop da pastoci da sauran wakilan mabiya cocin darikar Angalika daga sassa daban-daban na kasar, sun kammala wani babban taro da suka gudanar a garin Benin, babban birnin jihar Edo.

Inda suka tattauna batutuwan da suka shafi cocin nasu, da kuma wasu daga cikin muhimman al'amuran kasar.

Har mahalarta taron sun yi barazanar yanke zumunci da cocin Angalika na Ingila, dangane da batun auratayya a tsakanin mutane masu jinsi guda da madigo da kuma luwadi.

Har ila yau mahalarta taron sun yi kiran da a samarwa fulani burtaloli a yankunan kudu maso kudancin Najeriya, domin gujewa rikicin da ake tsakanin manoma da makiyayan.