Dokar ta-baci a wasu jihohin Amurka

Guguwa da dusar kankara
Image caption Guguwa mai karfin gaske da dusar kankara sun lullube arewa maso gabashin Amurka

Guguwa da dusar kankara ta fara lullube arewa maso gabashin kasar Amurka, inda aka kafa dokar ta-baci a jihohin Massachusetts, da Rhode Island, da New York, da Connecticut, da Maine.

An gargadi miliyoyin mazauna yankunan da su zauna a gida, yayin da dubun-dubatar mutane za su kasance babu wutar lantarki.

Magajin garin birnin New York Michael Bloomberg ya ce:

“Ku kauracewa tituna, ku kauracewa motocinku, ku kuma zauna a gida a daidai lokacin da wannan guguwa mai tafe da dusar kankara ke wucewa”.

An soke tashin dukkanin jiragen sama, musamman wadanda ke tashi a manyan filayen jiragen sama uku da ke New York.

Karin bayani