A tsaurara ka'idojin haraji —Action Aid

Rahoton Action Aid
Image caption Rahoton da Action Aid ta fitar ya yi nazari a kan illar daukewa wani kamfanin sukari biyan haraji a Afirka

Kungiyar agaji ta Action Aid mai yaki da talauci—wadda ke da shelkwata a Birtaniya—ta yi kira ga shugabannin kasashen duniya wadanda za su halarci taron manyan kasashen duniya bakwai, wato G7, a watan yunin wannan shekarar, su dauki kwakkwaran mataki na karfafa ka'idojin biyan haraji na duniya.

A wani rahoto da ta fitar yau, kungiyar ta Action Aid ta yi ikirarin cewa a kasar Zambia, ta hanyar yafe haraji a bisa tanade-tanaden doka, wani babban kamfanin sarrafa abinci na kasa-da-kasa yana biyan harajin da bai kai wanda daya daga cikin leburorinsa ke biya ba.

Kungiyar ta ce harajin da akan yafewa kamfanin mai suna Associated British Foods zai iya samar da karin gurabe 48,000 ga yara a makarantun Zambia duk shekara.

Da ya ke mayar da martini, kamfanin ya ce Zambia tab a daga masa kafa ne da niyyar karfafa masa gwiwa, kuma tun daga shekarar 2008 ya zuba jarin fam miliyan dari da hamsin a kasar, ya kuma samar da ayyukan yi ga mutane fiye da dubu biyar.

Tuni dai gwamnatin Birtaniya, wadda ita ce mai masaukin taron, ta ce tana so a sanya batun harajin da manyan kamfanonin kasashen duniya ke biya a ajandar taron.

Karin bayani