Almundahana: Ministar ilimi ta Jamus ta yi murabus

Image caption Annette Schavan, mistar ilimin Jamus da tayi murabus

Ministar Ilmi ta Jamus Annette Schavan a yi murabus sakamakon zargin satar fasaha a kundin digrinta na uku.

Matakin ya zo ne kwanaki hudu bayan da Jami'ar Dusseldof ta kwace digrin digirgir da ta baiwa Misis Schavan inda ta zarge ta da kwafar wasu sassa na kundin digirin daga wasu shekaru talatin da suka wuce.

Ita dai Annette Schavan aminiya ce ta kurkusa da shugabar gwamnatin Angela Merkel.

Wannan shine karo na biyu da minista a gwamnatin Merkel da matsala game da zargin satar fasaha.

Ms Schavan ta musanta zargin ta kuma ce za ta kai karar jami'ar kotu akan wannan lamari.