Polio: Gwamnatin Najeriya ta yi tir da kisa

Ana diga rigakafin Polio a Najeriya
Image caption Ana diga rigakafin Polio a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya yi Allah-wadai da kisan wadansu ma’aikatan riga-kafin cutar shan-inna—wato polio—a birnin Kano dake arewacin kasar.

A wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mai ba shi shawara a kan al'amuran yada labarai, Reuben Abati, Shugaba Jonathan ya yi kokarin kwantarwa iyalan mamatan hankali da cewa gwamnati ba za ta bari sadaukar da rayukan da suka yi ta tashi a banza ba.

A cewarsa gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa don tabbatar da cewa an kammala aikin da suka sa a gaba na kawar da cutar ta polio cikin nasara.

Haka zalika, sanarwar ta ce yayin da gwamnati ke ci gaba da kokarin zakulo wadanda suka aikata kashe-kashen, shugaban na Najeriya ya bayar da umarnin samarwa da kuma kara tsaurara matakan tsaro ga jami'an kiwon lafiya nan take a yankunan da ke fama da rikice-rikice.

Ita ma Kungiyar Likitoci ta Najeriya ta yi jimamin mutuwar jami'an kiwon lafiyar sannan ta ce a idonta wadanda suka rasa rayukan nasu jarumai ne na yakin da ake yi da cutar polio a Najeriya.

Su ma Asusun Tallafawa Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO), sun bi sahun gwamnatin ta Najeriya wajen yin Allah-wadai da lamarin, suna masu cewa hare-haren bala'i ne kan bala'i ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

A wata sanarwa da suka fitar ta hadin gwiwa, UNICEF da WHO sun kuma ce wannan ci baya ne ga yunkurin da ake yi na ceto rayukan al'umma, musmman ma kananan yara, sannan suka sha alwashin ci gaba da yin aiki tare da gwamnati da al'ummar Najeriya a yunkurinsu na inganta lafiyar jama'ar kasar.

Ranar Juma'a ne dai wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hare-hare a kan wadansu cibiyoyin kiwon lafiya biyu da ke birnin Kano, inda suka kashe akalla ma'aikatan allurar polio mata su tara.

Karin bayani