Mutane talatin da shida sun mutu a India

Kumbh Mela
Image caption Turmutsutsu yayin bikin ibada na Kumbh Mela ya haddasa mutuwa a India

Jami'an ’yan sanda a India sun shaidawa BBC cewa kimanin mutane talatin da shida ne suka rasa rayukansu a wata tashar jirgin kasa da ke kusa da daya daga cikin manyan wuraren da ake gudanar da bikin addini na Kumbh Mela.

Da yawa daga cikin wadanda abin ya rutsa da su mata ne.

Al’amarin ya faru ne a lokacin da wata gadar kafa da ke Allahabad ta rufta.

Al'ummar kasar ta India na yin wanka a cikin ruwan Ganges da Yamuna domin wanke zunubansu, kuma suna daukar ranar Lahadi ranar da ta fi albarka albarka a lokacin bikin.

Karin bayani