Ana artabu a birnin Gao na arewacin Mali

Sojojin Faransa a Gao
Image caption Sojojin Faransa sun kasa sun tsare a Gao

Fada ya sake barkewa a kewayen garin Gao na arewacin Mali, inda ’yan tawaye masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci suka kaddamar da wani hari na ba-zata ranar Lahadi.

An bayar da rahoton jin karar fashewar wani abu da sanyin safiyar Litinin a birnin—wanda shi ne birni mafi girma a arewacin Mali—sa'o'i bayan 'yan tawaye sun gwabza kazamin fada da dakarun Mali da na Faransa.

Tun da farko dai sojojin na Mali da na Faransa sun samu nasarar kwantar da kurar harin cikin dare.

Fadan na ranar Lahadi dai ya biyo bayan wadansu hare-haren kunar bakin wake ne da ’yan tawayen suka kai a kan wani wurin binciken ababen hawa a ranakun Juma'a da Lahadi.

Wannan ne karo na farko da aka ga ’yan tawayen a titunan Gao, wanda shi ne birni mafi girma a arewacin Mali, tun bayan da aka fatattake su a watan jiya.

A ranar Lahadin an yi ta jin karar fashewar abubuwa da harbe-harben bindiga lokacin da ’yan tawayen suka kai harin.

Wani dan jaridar kasar Faransa ya yi bayyana yadda al’amarin ya faru:

“Muna daf da karasawa Dandalin Shari'a ke nan sai muka ji luguden harsasai. Ban sani ba ko motocinmu aka harba, amma dai babu shakka harbin ya sauka a kan wani bango da ke bakin titi, saboda haka muka kara wuta.

“A guje muka keta sha-tale-talen zuwa Dandalin na Shari'a har muka kai inda sojojin Mali suke a daya bangaren. Nan take muka kara jin harbe-harbe yayinda ’yan tawayen suka yi yunkurin ketowa ta cikin dandalin”.

Wakilin BBC a Gao ya ambato rundunar sojin Faransa na cewa ’yan tawayen da suka kaddamar da harin ba su fi su goma sha biyu ba—abin da ya bayar da mamaki ganin cewa an kwashe sa'o'i ana gwabzawa a titunan birnin.

Masu aiko da rahotanni sun ce 'yan tawayen, wadanda ga alama sun kaddamar da yakin sari-ka-noke ne, sun sha alwashin ci gaba da kai irin wadannan hare-haren, kuma jama'a na fargabar wadansu daga cikinsu na nan a labe a cikin birnin.

Kungiyar masu tsattsauran ra'yin addinin Musulunci ta Hada kan Al'umma da Jihadi a Yammacin Afirka, wato MUJAO, ta ce ita ce ta kai harin.

Karin bayani