An kashe likitoci 'yan Korea ta arewa a Potiskum

Image caption Taswirar Najeriya

An kashe likitoci uku 'yan ƙasar Korea ta arewa a garin Potiskum dake jihar Yobe a rewacin Najeriya, kuma rahotanni na cewa an yiwa ɗaya daga cikinsu yankan rago.

An dai kai harin ne a gidan da likitocin ke aiki da babban asibitin garin.

Daya daga cikin likitocin dai an yanke masa kai, yayin da aka yanka sauran a wuya.

Cikin 'yan shekarun baya-bayan nan ne dai ƙasar Korea da Arewar ta aiko da Likitocin sha takwas da ma wasu Injiniyoyi, a bisa yarjejeniyar da suka ƙulla tsakaninsu da gwamnatin jihar Yobe game da harkokin kiwon lafiya.

Har yanzu dai babu wanda ya dau alhakin aikata wannan kisa, amma kungiyar nan da ake kira Boko Haram ta hallaka daruruwan mutane a arewacin Najeriya cikin shekaru hudun da suka gabata.