Manyan sojojin Guinea sun mutu a hatsarin jirgi

Taswirar Kasar Guinea
Image caption Jirgi dauke da sojojin Guinea ya yi hatsari

Hafsan hafsoshin sojin kasar Guinea, Kalifa Dialo ya rasa ransa a wani hadarin jirgi a kusa da Monrovia, babban birnin kasar Liberia, tare da wasu kusoshin sojin kasar akalla su biyar.

Jirgin na su ya fadi ne a kusa da babban filin jiragen sama na kasar.

Magdela Cooper ta shaida hatsarin jirgin kuma tace 'munga jirgin, mutanen ciki su na ta ihu su na neman taimako, amma ba abin da za su iya amfani da shi wajen fasa tagar jirgin ta bude'.

Ministan tsaro na Guinea ya ce ana gudanar da bincike kan musabbabin hadarin jirgin.

Janar Diallo wani na hannun daman shugaban kasar Guinea ne, Alpha Code, kum shi ke da alhakin gyara tsarin sojojin kasar.

Tawagar na kan hanyarta ne na zuwa Conakry domin halartar bikin ranar sojoji a Liberia.

Karin bayani