An kama 'yan jarida biyu a Kano kan Polio

Polio
Image caption Kimanin masu allurar shan inna tara aka kashe a wani harin 'yan bindiga a Kano

An kama wasu 'yan jarida biyu a jihar Kano ta Najeriya saboda kisan da aka yiwa wasu mata ma'aikatan allurar rigakafin cutar shan inna (polio) su tara ranar Juma a garin, kamar yadda 'yan sanda suka ce.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano Ibrahim Idris ya shaida wa BBC cewa za a caji 'yan jaridar da aikata kisan kai.

Ya yi zargin cewa sun ingiza jama'a su kauracewa allurar rigakafin ta hanyar watsa wani shiri a gidan rediyon Wazobia FM.

Ra'ayin jama'a ya rabu kan allurar a arewacin Najeriya; yayin da wasu ke ganinta a matsayin wata makarkashiya ta rage yawan al'umar Musulmi, wasu kuma na ganin allurar bata da wata illa.

Sheikh Ahmad Muhammad Gumi na jihar Kaduna, na daya daga cikin malaman addinin da ke ganin allurar bata da wata illa, kuma ya kamata jama'a su bayar da 'ya'yansu domin ayi musu.

Ana ganin irin wannan cece-kucen da ake yi na daya daga cikin dalilan da ya sa cutar ta shan inna ta zamo kadangaren bakin tulu a wasu kasashe uku kacal a duniya.

Shirin Sandar Girma....

An samu bullar cutar sau 121 a Najeriya bara, idan aka kwatanta da 58 da aka samu a Pakistan da kuma 37 a Afghanistan, kamar yadda cibiyar yaki da cutar ta Global Polio Eradication Initiative ta bayyana.

Shugaban gidan rediyon na Wazobia Sanusi Bello Kankarofi ya ce 'yan sanda suna tsare da kama wani mai gabatar da shiri da kuma mai nemo labarai, tare da mutumin da aka yi hira da shi a shirin.

An saki dan jarida na uku bayan da aka yi masa tambayoyi, a cewar Mr Kankarofi.

Shirin Sandar Girma na Wazobia wanda ke da farin jini, ya mayar da hankali ne kan wani mutum da aka yi zargin mahukunta sun tilasta masa mika yaransa domin a yi musu allurar rigakafin ta shan inna.

Kankarofi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mahaifin yara yana daya daga cikin wadanda aka tsare.

Karin bayani