An kai wasu 'yan jarida kotu a Kano kan Polio

Polio
Image caption Kimanin masu allurar shan inna tara aka kashe a wani harin 'yan bindiga a Kano

Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta Najeriya ta gurfanar da wasu 'yan jarida biyu a gaban kotu bayan kisan wasu mata ma'aikatan allurar cutar shan inna (polio) su tara ranar Juma a garin.

An zarge su da hada baki da kuma ingiza mutane su yi tashin hankali.

Gidan rediyion Wazobia ya watsa ra'ayoyin wasu mutane da suke adawa da shirin allurar rigakafin na Polio a jihar ta Kano, kwanaki biyu kafin kai harin.

Rahotanni sun ce kwamitin kare hakkin 'yan jarida wanda ke da hedkwata a birnin New York na Amurka, ya ce ya "kadu" game da batun tsarewa da kuma cajar 'yan jaridar.

Ra'ayin jama'a ya rabu kan allurar a arewacin Najeriya; yayin da wasu ke ganinta a matsayin wata makarkashiya ta rage yawan al'umar Musulmi, wasu kuma na ganin allurar bata da wata illa.

Sheikh Ahmad Muhammad Gumi na jihar Kaduna, na daya daga cikin malaman addinin da ke ganin allurar bata da wata illa, kuma ya kamata jama'a su bayar da 'ya'yansu domin ayi musu.

Ana ganin irin wannan cece-kucen da ake yi na daya daga cikin dalilan da ya sa cutar ta shan inna ta zamo kadangaren bakin tulu a wasu kasashe uku kacal a duniya.

Shirin Sandar Girma....

An samu bullar cutar sau 121 a Najeriya bara, idan aka kwatanta da 58 da aka samu a Pakistan da kuma 37 a Afghanistan, kamar yadda cibiyar yaki da cutar ta Global Polio Eradication Initiative ta bayyana.

Tun da farko kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano Ibrahim Idris, ya shaida wa BBC cewa za a tuhume su da aikata kisan kai.

Amma sai masu gabatar da kara suka zo da tuhumar da bata kai wannan ba a lokacin da aka isa kotu - inda aka tuhume su da tayar da hankali da kawo cikas ga tsarin aikin gwamnati, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Shugaban gidan rediyon na Wazobia Sanusi Bello Kankarofi ya shaida wa BBC cewa 'yan sanda suna tsare da wani mai gabatar da shiri da kuma mai nemo labarai, tare da mutumin da aka yi hira da shi a shirin.

An saki dan jarida na uku bayan da aka yi masa tambayoyi, a cewar Mr Kankarofi.

Shirin Sandar Girma na Wazobia wanda ke da farin jini, ya mayar da hankali ne kan wani mutum da aka yi zargin mahukunta sun tilasta masa mika yaransa domin a yi musu allurar rigakafin ta shan inna.

Kankarofi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mahaifin yara yana daya daga cikin wadanda aka tsare.

Karin bayani