Red Cross zata gaggauta tura kayan agaji Mali

Kungiyar Red Cross
Image caption Ana shirin kai agaji Mali

Kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce zata gaggauta aikewa da kayayyakin agaji ga 'yan kasar Mali su dubu shida da suka tserewa fadan da ake a arewacin kasar.

Kungiyar ta Red Cross ta ce abincin da 'yan gudun hijirar ke da shi ba shi da wani yawa, kuma suna fakewa ne karkashin bishiya da ababan hawa da su ka lalace.

Mutanan sun tsere ne daga garuruwan Gao da Kidal zuwa wani kauye dake kusa da kan iyakar Algeria.

Dubban mutane ne aka tilastawa tserewa fadan, yayin da dakarun Faransa da na Mali ke kokarin fatattakar 'yan tawaye.

Karin bayani