'Yan damfara na cutar masu neman aiki a Najeriya

Image caption 'Yan sandan Najeriya

A Najeriya, rahotanni na cewa 'yan damfara na cutar masu neman ayyukan yi, ta yi musu alkawarin samun aiki ta hanyar intanet.

Wadansu mutane da ke neman ayyukan yi sun shaidawa BBC cewa 'yan damfarar na fakewa ne da cewa suna wakiltar kamfanoni ko hukumomin kasashen waje, irin su Majalisar Dinkin Duniya, kuma za su bukaci mutane su aika da takardun neman aiki da kudi; amma da zarar an yi hakan sai su bace.

Hakan dai na jefa dubban masu neman aiki fadawa hannun irin wadannan batagarin.

Sai dai yanzu haka 'yan sanda sun kama wadansu 'yan damfarar don dakile matsalar.

Karin bayani