Wanene zai gaji Paparoma?

Image caption Paparoma Benedict

Kwana guda bayan shugaban mujami'ar Roman Katolika, Paparoma Benedict, ya sanar cewa zai yi murabus, yanzu hankula sun karkata ne kan wanda zai gaje shi.

Shi dai Benedict shi ne Paparoma na farko da ya taba yin murabus cikin shekaru fiye da dari shida.

Ana ganin cewa mutumin da zai gaje shi zai fito ne daga yankin Latin Amurka, inda a can ne kusan kashi arba'in cikin dari na kiristoci mabiya darikar Katolika suke.

Sai dai akwai wadansu a nahiyar Afrika da suka fito daga Ghana da Nigeria da ake ganin suna iya samun wannan mukamin.

Karin bayani