Sojojin Thailand sun kashe mutane 20

Image caption Taswirar kasar Thailand

Sojoji a kasar Thailand sun ce sun kashe 'yan wata kungiyar da ke dauke da makamai guda 20 wadanda suka kaddamar da hare-hare a wani sansanin soji da ke kudancin kasar.

Kakakin rundunar sojin kasar, Kanar Pramote Promin, ya ce wadansu 'ya'yan kungiyar sanye da kaya irin na soji sun kai hari kan sansanin sojin da tsakar dare.

Dubban mutane ne dai suka hallaka cikin shekaru goma da suka gabata tun bayan wadansu 'yan aware wadanda suka fito daga kudancin kasar suka kaddamar da hare- hare.

Karin bayani