'Yan adawar Zimbabwe sun koka kan cin zarafin Jama'a

Zimbabwe
Image caption Zargin cin zarafin jama'a a Zimbabwe

'Yan adawa a kasar Zambia na kira ga kungiyar kwamanwelz da ta gudanar da bincike kan zargin cin zarafin jama'a da ake zargin gwamnatin Zambia da aikatawa.

A lokacin wani taron manema labaru a birnin Johannesburg, kawancen kungiyoyin fafutukar kare dimokradiyya sun ce akwai shaidu kwarara na cin zarafi da ake yi wa gwamnatin shugaba Michael Sata, wadda aka zaba a bara.

'Yan adawa a kasar Zambia sun yi kira ga kungiyar kasashe rainon Ingila ta binciki cin zarafin bil Adama wanda ake zargin gwamnatin Zimbabwe da aikatawa.

'Yan adawar sun mika kundin rahoto mai shafi 40 ga sakataren kungiyar kasashe rainon Ingila Commonwealth tare da bukatar a nada jakada nma musamman domin ya binciki zarge-zargen.

Karin bayani