Alkalan wasa sun fusata manajan Celtic

Juventus da celtic
Image caption Wasan Juventus da kuma Celtic

Kocin kungiyar kwallon kafa na Celtic, Neil Lennon ya nuna bacin rai ga alkalan wasa, bayan kungiyar Juventus ta lallasa Celtic da ci uku da nema, a gasar zakarun Turai.

'Yan wasan Juventus, wanda Celtin ta dauki bakuncinsu, sun nuna karfi sosai a karawar, kuma alkalin wasan wanda dan kasar Spaniya ne, Alberto Undiano Mallenco ya ki ba da bugun fenariti.

"An yi ta nuna musu karfi, duk da cewa ba wasan zari ruga bane" a cewar Lennon.

"Yan wasanmu sun rinka fadawa akalin wasa ya sa ido, amma babu abin da ya yi game da bukatarmu"

Sai dai kocin Juventus, Antonio Conte bai shiga cikin ce-ce-ku-cen da ake yi ba, bayan da aka fada masa abin da Lennon ya ce game da alkalan wasan.

Kungiyar ta Celtic ta sha kaye a karawar da suka yi da Juventus, inda Alessandro Matri ya zura kwallon farko a ragar Celtic, sai kuma kwallayen da Claudio Marchisio da kuma Mirko Vucinic suka kara a ragar abokan karawarsu, bayan hutun rabin lokaci na farko.

Karin bayani