Shirin samar da kasuwar da ta fi kowacce girma a duniya

Taron kungiyar Tarayyar Turai
Image caption Yarjejeniyar kasuwanci da zuba jari a Tarayyar Turai

Amurka da Tarayyar Turai sun ce za su fara tattaunawa kan wata yarjejeniyar kasuwanci da zuba jari, wadda za ta iya samar da kasuwar da ta fi kowacce girma a duniya.

A cikin wata sanarwar hadin guiwa, bangarorin biyu sun ce yarjejeniyar za ta bunkasa tattalin arzikin Tarayyar Turai da dala biliyan 116 nan da shekara ta 2027.

Haka itama Amurka sun ce za ta samu bunkasar tattalin arzuki kamar haka.

"Ina bada sanarwar cewa za mu kaddamar da wata cikakkiyyar tattaunawa kan kasuwanci da zuba jari tsakaninmu da Tarayyar Turai," a cewar Shugaba Obama na Amurka.

Shugaban Hukumar Tarayyar Turan, Jose Manual Barroso ya kwatanta yarjejeniyar da cewa za ta sauya al'amura.

Karin bayani