An soma kwashe kasa mai gubar dalma a Zamfara

Masu ayyukan hakar ma'adinai sun jera hajojinsu
Image caption Masu ayyukan hakar ma'adinai sun jera hajojinsu

An soma kwashe kasa mai gubar dalma a karamar hukumar Bagega dake jihar Zamfara, inda akala yara 1,500 ke bukatar kulawa sakamakon gubar dalmar.

Kamfanin da aka ba kwangilar kwashe kasar, Terragraphics ya ce tun ranar lahadi ya aika da ma'aikatansa zuwa jihar, kuma a ranar Talata ne aka soma aikin kwashe gurbataciyyar kasa .

Sai dai Simba Tirima injiniya a kamfanin ya ce matakin da za a dauka don magance daukacin matsalar, ita ce samar da dokokin da zasu rinka sa ido kan kananan masu hakar ma'adinai dake hakar gwal, ba wai a haramta musu sana'ar baki daya ba.

A watan janairun daya gabata ne dai, gwamnatin Najeriya ta amince da bada kudi naira miliyan 850 daga asusun kula da muhalli, domin gudanar da aikin kwashe kasar mai gubar dalma a jihar ta Zamfara.

Haka kuma a ranar Talata ne kungiyar agaji ta likitocin, wato MSF ta soma gwajin jinin yara 'yan kasa da shekaru biyar a wuraren da matsalar ta shafa a Bagega.

Garuruwa a karamar hukumar ta Bagega sun shafe tsawon lokaci suna zaman jira a kwashe kasar, tun shekarar 2010, lokacin da yara 400 suka rasa rayukansu, kuma matsalar ta jefa rayuwar dubban mutane cikin hadari.