Kamfanonin jiragen sama za su hade

Image caption Jiragen American Airlines da US Airways

Hukumomin gudanarwa na kamfanonin sufurin jiragen sama na American Airlines da US Airways sun gana domin kulla yarjejeniyar dunkulewa waje guda.

Yarjejeniyar za ta kai ga samar da babban kamfanin sufurin jiragen sama mafi girma ta fuskar yawan fasinjoji a duniya.

Ana sa ran darajar kamfanin za ta kai ta kimanin dala biliyan 11.

Ana kulla yarjejeniyar ce watanni goma sha hudu bayan kamfanin American Airlines ya bayyana cewa ya talauce, kuma masu bin sa bashi sun tilasta masa cewa ya fara tunanin hadewa da wani kamfanin.

Sabon kamfanin zai rika amfani da sunan American Airlines, amma shugaban kamfanin US Airways, Doug Parker, ne zai jagorance shi.

Karin bayani