Tarayyar Turai na so a yi bincike kan naman doki

Image caption Kwamishinan Lafiya na Tarayyar Turai, Tonio Borg.

Majalisar zartarwar Tarayyar Turai ta bayar da shawarar yin gwaje-gwaje domin magance matsalar sayar da naman doki a matsayin naman shanu.

Kwamishina mai kula da harkar noma na Tarayyar Turai, Tonio Borg, ya ce ya kamata a rika gudanar da gwaje-gwajen da za su nuna cewa naman shanu daban yake da naman doki.

Majalisar ta bukaci a rika gwada naman doki don tabbatar da cewa ba ya dauke da magungunan da ake bai wa dabbobi.

Ministan noma na kasar Ireland, Simon Coveney, ya ce matsalar da ake fuskanta ta kasashen da ke nahiyar Turai ce wacce ke bukatar a warware ta a nahiyar.

Kasashen Turai da dama sun gano cewa akasarin abincin gwangwanin da ake sayarwa na dauke da naman doki, wanda kuma ake sayarwa a matsayin naman shanu.

Karin bayani