Jacob Zuma na fuskantar kalubale

Image caption Jacob Zuma

A ranar Alhamis ne shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta Kudu zai gabatar da jawabin sa na shekara-shekara a yayin da za a bude majalisar dokokin kasar a birnin Cape Town.

Jawabin nasa na zuwa a lokacin da kasar ke fuskantar kalubale da dama.

Zanga-zangar da aka rika yi a wajen hakar ma'adinan kasar ta sanyaya gwiwar masu zuba jari; kazalika a badi ne za a gudanar da zaben shugaban kasar.

Shugaba Jacob Zuma ya yi alkawura da dama a shekaru hudun da suka gabata, sai dai wadanda ya cika ba su taka kara sun karya ba.

Gwamnatin Zuma ba ta tsinana komai ba

Ya karfafa matsayinsa a jam'iyar African National Congress ANC, wacce ke mulkin kasar, hakan ne ma ya sanya a watan Disamba, ya yi nasarar samun wa'adi na biyu a matsayin shugaban jam'iyar.

Sai dai ana zargin gwamnatinsa da gaza yin katabus wajen inganta muhimman fannoni kamar ilimi, da kiwon lafiya, da samar da ayyukan yi.

Haka kuma ya gaza magance matsalolin tsaro, da na cin hanci a kasar.

Tattalin arzikin kasar yana tafiyar hawainiya.

Sai dai gwamnatin Afirka ta Kudu na fatan bunkasa tattalin arzikin kasar bayan da ta gabatar da wani tsari na samar da ci gaban kasa, wanda dukkan jam'iyun kasar suka amince da shi, kodayake ba a fara aiwatar da shi ba.

Karin bayani