Jacob Zuma ya yi kiran kawo karshen ayyukan fyade

  • 14 Fabrairu 2013
Jacob Zuma
Image caption Fyade a Afirka ta Kudu

Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya yi amfani da jawabinsa na shekara-shekara wurin kiran a hada kai wurin kawo karshen ayyukan fyade a kasar.

Yana nuni ne da wata yarinya 'yar shekara sha bakwai da ta mutu bayan da wasu gungun mutane suka yi mata fyade a farkon watan nan.

Yace irin wannan dabi'a ba ta dace ba kuma ba ta da gurbi a rayuwar jama'ar kasar.

Mr Zuma ya kuma ce bai kamata a sake maimaita kisan da aka yiwa ma'aikatan hakar ma'adinai fiye da arba'in a Marikana ba a bara.

Sannan ya yi kira ga mutane da su yi amfani da damar da suke da ita ta yin zanga-zanga cikin lumana da kuma tsari.

Karin bayani