Kotu ta bukaci a tsare Shugaba Al Bashir

Omar Al Bashi na Sudan
Image caption Ana tuhumar Al Bashir da aikata laifukan yaki

Kotun manyan laifuka ta duniya ta bukaci Kasashen Chadi da Libya da su tsare Shugaba Omar al Bashir na Sudan, sannan a tusa keyarsa domin ya fuskanci shari'a, idan har ya ziyarci Kasashen biyu a karshen mako

Wannan umarni shine yunkurin Kotun dake Hague na baya bayan nan na ganin cewa an tsare shugaban

Ana dai zargin sa da shirya kisan kare dangi da kuma aikata laifukan yaki a yankin Darfur na Sudan

Kasashen Chadi da Kenya da wasu kasashen Afirka da dama sun karbi bakwancin Mr Bashir, duk da cewa dukkanin su sun amince da kotun manyan laifukan

Karin bayani