'Ana musgunawa 'yan jarida'

Image caption Wadansu ma'aikatan watsa labarai

Wani rahoto da Kwamitin da ke kare hakkin 'yan jarida na duniya da ke Amurka ya fitar ya ce akalla dan jarida daya ne ke rasa ransa a kowanne mako sakamakon muzgunawar da ake yi wa ma'aikatan kafofin sadarwa a duniya.

Kwamitin ya ce sakamakon binciken da ya gudanar a bara ya nuna cewa 'yan jarida fiye da 230 ne ke tsare a gidan yari sakamakon gudanar da ayyukansu.

Kwamitin ya kara da cewa kimanin 'yan jarida talatin da biyar ne suka bace a shekarar 2012.

Wannan dai shi ne bincike mafi muni da Kwamitin ya gudanar tun bayan da ya fara gudanar da irin wadannan bincike a shekarar 1990.

Karin bayani