Kotu a Kenya ta baiwa Uhuru Kenyatta damar tsayawa zabe

Uhuru Kenyatta da William Ruto
Image caption Uhuru Kenyatta zai iya tsayawa takarar zaben Kasar Kenya

Yayinda ya rage makonni biyu, a yi zaben shugaban kasar Kenya, babbar kotu ta ce ba za ta iya hana daya daga cikin na gaba - gaba a takarar, Uhuru Kenyatta da mataimakinsa, tsayawa takarar ba.

Alkalin Kotun Mbogholi Msagha ne ya karata hukuncin kotun inda ya ce 'ya zuwa ranar yau, an kammala batun tsayawa takarar mutum na 3 da na 4 da ake kara. Game da korafin dake gabanmu, babu wani da ya kalubalanci batun takarar tasu.Tuni mun warware batun shara'ar da ya shafi zaben Shugaban kasa, kuma ba za mu kara cewa kome ba'.

Mr Kenyatta da William Ruto na fuskantar tuhumar aikata laifukan cin zarafin jama'a a kotun manyan laifuka ta duiya a Hague, game da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekaru 5 da suka wuce da aka yi takaddama kansa.

Dukanin mutanen dai sun musanta zargin.

Magoya bayansu sun yi ta murna bayan da Alkalan babbar kotun ta yanke hukuncin cewar ba ta da hurumin hanawa mutanen biyu tsayawa takara.

Karin bayani