Rahoto kan yadda yanayi a Najeriya zai kasance a 2013

Ambaliyar ruwa a Najeriya
Image caption An bada rahotan yanayi a Najeriya

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NIMET ta sanar da cewa a wannan shekara ta 2013 ruwan sama ba zai yi yawa ba, kamar na shekarar data gabata, kuma za' a samu karancin ruwan saman a wasu jahohi.

Hukumar ta sanar da hakan ne a hasashen damunar bana da ta fitar a yau a Abuja.

Sai dai kuma hukumar ta ce a yi hattara, don kuwa tace za' a iya samun iska mai karfi.

Shi dai sakamakon wannan hasashe zai iya taimakawa wajen ganin an yi tsarin tattalin arziki, da kuma bunkasa rayuwar al'umma yadda ya dace.

A bara dai an samu mummunar ambaliyar ruwa a wasu sassan Najeriya.

Karin bayani