Oscar Pistorius ya yi kuka a kotu

Oscar Pistorius
Image caption Mr Pistorius ya yi fice a fagen wasannin duniya

Zakaran tseren wasan nakasassu na Afrika ta Kudu Oscar Pistorius, ya yi kuka a kotu bayan da masu gabatar da kara suka tuhume shi da "kisan kai" bayan da aka samu gawar budurwarsa a gidansa.

An harbe Reeva Steenkamp - wacce ke tallan kayan kaya a gidansa da ke birnin Pretoria ranar Alhamis.

Mr Pistorius ya rike kansa da hannu sannan ya rushe da kuka bayan da aka karanto masa laifin da ake tuhumarsa da aikata wa a wata kotun Majistiri.

An dage bukatar da ya gabatar ta neman beli har zuwa ranar Talata.

Kafin sannan za a ci gaba da tsare Mr Pistorius, mai shekaru 26, a hannun 'yan sanda.

Karin bayani