Makeken dutse ya wuce kusa da duniya

Makeken dutse
Image caption Makeken dutsen da yai wuce ta kusa da duniya

Wani makeken dutse da ya kai girman filin kwallo ya wuce ta kusa da duniya da kusancin kilomita dubu ashirin da takwas—kusancin da ya fi na taurarin dan adam din da tashoshin talabijin da masu hasashen yanayi ke amfani da su—salim-alim.

Sai dai masana kimiyya sun ce ba shi da alaka da wata tauraruwa mai wutsiya da ta kone a sararin samaniyar Rasha, ta kuma lalata gine-gine da dama.

Mazauna garin Chelyabinks na Rasha—inda tauraruwar ta tarwatse—sun bayyana yadda suka ga wani haske da ba su taba ganin irinsa ba, sannan daga bisani suka ji karar fashewar wani abu.eteor

Karin bayani