Ana zaben shugaban kasa a Cyprus

'Yan takarar shugabancin kasar Cyprus
Image caption 'Yan takarar shugabancin kasar Cyprus

An bude rumfunan zabe a Cyprus don zaben sabon shugaban kasa.

Batun matsalar tattalin arziki ne dai ya kankane yakin neman zabe.

Wannan zabe ne dai mafi muhimmanci ga kasar ta Cyprus a shekaru da dama saboda yadda ake matukar bukatar shugaban da zai jagorance ta ta fice daga matsalar ta koma-bayan tattalin arziki.

Batun da duk wanda ya yi nasara zai fi mayar da hanaklai a kai shi ne kammala wani shiri na karbo tallafi daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) da kungiyar Tarayyar Turai bayan da bankunan kasar suka shiga tasku sakamakon alakar bashin da ta shiga tsakaninsu da Girka.

Dan takarar masu matsakaicin ra’ayin mazan jiya Nicos Anastasiades ne ke kan gaba a kuri’ar jin ra’ayin jama’a; amma tazararsa da wanda ke rufa masa baya ba ta kai yadda za a kaucewa zuwa zagaye na biyu ba a zaben a makon gobe.

Sabon shugaban kasar zai kuma sha matsin lamba a kan ya taimaka don sake dinke tsibirin, wanda tun shekarar 1974 ya ke dare gida biyu tsakanin Turkawa da Girkawa.

Gano dimbin iskar gas a kasar kwanan baya ya dasa kyakkyawan fata a zukatan al'umma; sai dai kuma karuwar rashin aikin yi da koma-bayan tattaklin arziki babban kalubale ne ga duk wanda ya yi nasara.

Karin bayani