Karzai zai hana sojin Afghanistan neman dauki

Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan
Image caption Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan

Shugaba Hamid Karzai ya ce ba za a bari dakarun tsaron Afghanistan su bukaci a kai masu dauki da jiragen yaki a yankunan zaman jama'a ba.

Sanarwar ta zo ne kwanaki bayan da aka kashe wasu fararen hula 10 a wani harin da aka kai ta sama a lardin Kunar na gabacin kasar .

Kodayake a halin yanzu dakarun Afghanistan ne ke jagorantar galibin farmakin da suke neman taimako daga dakarun da kungiyar tsaro ta NATO ke jagoranta don kai hare hare ta sama.

Shugaba Karzai ya ce zai fitar da wata doka a gobe lahadi.

Ba a sa ran dakarun tsaro na NATO su mayar da martani game da sanarwar har sai lokacin

Karin bayani