Wata Kungiyar kabilar Igbo ta ayyana kafa Jamhuriyar Biafra

Wasu masu fafautikar kafa Biafra da tutucin kasar
Image caption Wasu masu fafautikar kafa Biafra da tutucin kasar

Kungiyar nan mai suna Biafra Zionist Movement mai fafutikar kafa kasar yan kabilar Igbo zalla a Najeriya ta kaddamar da abun da ta kira ''Gwamnatin jamhuriyyar Biafra'' a birnin Enugu.

Kungiyar ta ambata sunayen wasu fitattun 'yan kabilar Igbo da ke rike da manyan mukamai a gwamnatin Najeriya, kamar su Cif Anyim Pius Anyim da Ngozi Okonjo-Iweala da Dezanie Allison Madueke a matsayin kusoshin gwamnatinta.

Kungiyar ta bukaci wadannan mutane da su karbi mukaman nan da mako guda, haka kuma ta umurci jami'an tsaron tarayyar Najeriya da su kwashe ya -nasu - ya -nasu su fice daga yankin nan da makunni biyu masu zuwa.

A watan Nuwamban bara ne dai wannan kungiya ta bayyana kafuwar jamhuriyar, al'amarin da ya sa rundunar 'yan sandan jihar Enugu ta kame shugabanni da 'ya'yan kungiyar fiye da dari daya. Kuma ta gurfanar da su a kotu, amma daga baya aka sako su a matsayin beli.