An dage sauraren neman belin Oscar Pistorius

Oscar Pistorius
Image caption Oscar Pistorius a kotu

An shaida wa wata kotu a kasar Afrika ta Kudu cewa an ji karar harbi, da ihun wata mata, sannan aka kara jin harbe-harbe, a gidan zakaran tseren nakasassu Oscar Pistorius, a daren da aka kashe budurwarsa Reeva Steenkamp.

Dansandan da ke bincike ya shaida wa zaman neman beli a kotun cewa, ya ji ana sa'insa, sai dai masu kare Pistorius sun ce mutumin yana da nisa da gidan da lamarin ya faru.

Pistorius ya ce, ya harbe Reeva ne bisa kuskure, bayan da ya yaci cewa dan fashi ne ya shiga gidan.

Mai binciken ya ce, yayi imanin cewa Mr Pistorius zai iya tserewa, don haka bai kamata a bayar da belinsa ba, yana mai cewa suna da shaidar cewa dan wasan na da asusun bankuna da kuma gidaje a kasashen ketare.

Wakilin BBC. ya ce, "lauyan dake kare Pistorious ya zargi 'yan sandan dake bincike da nuna son zuciya yana mai cewa gwajin da aka yi bayan rasuwar Ms Steenkamp ya nuna cewar ba a ga alamar bawali a mararta ba, abinda yayi daidai da bayanan Mr Pistorious cewa budurwarsa ta tashi ta shiga bandaki a cikin dare"

An dai dage sauraren neman bayar da belinMr Pistorius har sai gobe alhamis

Karin bayani