Paparoma Benedict ya yi fita ta ƙarshe

Paparoma Benedict XVI
Image caption Paparoma Benedict zai sanyawa dubban jama'a albarka a karo na karshe kafi ya sauka daga kujerarsa

Dubun dubatar jama'a ne suka hallara kuma suka yi jinjina ga Paparoma Benedict yau Lahadi, yayin da ya yi bayyana ta karshe a bainar jama’a kafin ya sauƙa daga muƙamin shugaban Cocin Roman Katolika a karshen wannan watan.

Wakilin BBC a Roma ya ce dole ta sa Vatican ta yi kwaskwarima ga dokokinta don zaben sabon paparoma—jami’an kula da zaben suna so su tabbatar an zabi wanda zai gaji Paparoma Benedict kafin bukukuwan Easter.

Paparoman ya leƙo ta tagar ɗakin karatunsa ya fuskanci dandalin St Peter, inda yake sanyawa masu ziyarar ibada albarka duk ranar Lahadi.

Daga nan kuma ya keɓe tare da manyan kadinal-kadinal domin yin addu’o’i har na tsawon kwanaki bakwai.

Karin bayani