Gwamnatin Bangladesh ta zartar da wata doka

Image caption Masu zanga-zanga a Bangladesh

Gwamnatin Bangladesh ta zartar da wata doka da ta ba gwamnati damar ɗaukaka kara a kan duk wani hukunci na Kotun Musamman a kan Laifukan Yaƙi ta ƙasar.

Matakin zai iya sanyawa a dinga yanke wa mutane hukunci mai tsanani.

An dai soma gagarumar zanga-zangar a birnin Dhaka ne jim kaɗan bayan kotun ta yankewa wani mai kaifin ra'ayin Islama hukuncin daurin rai da rai a farkon wannan watan saboda samunsa da aka yi da laifin tallafawa wajen kisa da azabtar da jama'a yayin yakin kwato 'yan cin kan Bangladesh.

Masu zanga-zangar dai suna kira ne a rataye mutumin da kotun ta samu da laifi.

Yaduwar zanga-zanga dai ya sawa gwamnati matsin lambar yin sauyi ga dokar.

Sauyin da aka yiwa dokar dai zai baiwa kotun ta musamman wani karfi na yin shari'a da kuma yanke hukunci akan kowacce kungiya ko jam'iyyar siyasa dake da hannu a yakin kwato 'yan cin kan kasar.

Sai dai masu suka cun ce, wannan sauyi ga dokokin bita da kulli ne ga jam'iyyar Jamaat Islami. wacce tayi adawa da samun 'yan cin kan Bangladesh daga Pakistan.