Najeriya: an sace 'yan ƙasashen waje 7 a Jama'are

A jihar Bauchi dake arewacin Nijeriya wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun sace wasu 'yan ƙasashen waje su bakwai dake aiki a ɗaya daga cikin manyan kamfanonin gine-gine a Nijeriya, wato Setraco.

Waɗanda suka kai harin sun kuma kashe mai gadi.

Maharan bisa bayanan da na samu sai suka shiga cikin gidan kwanan ma’ikatan dake wani wuri da ake ƙira Life Camp, ta hanyar fasa ginin da bama-bamai daga ta baya, suka kashe mai gadi ɗaya, kana suka sace ‘yan ƙasashen wajen su bakwai.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Bauchi, Alhaji Abubakar Ladan, ya tabbatar da sace 'yan ƙasashen wajen bakwai, amma ya ce kawo yanzu ba a iya tantance ko 'yan wadanne ƙasashe ne ba, kuma suna ci gaba da bincike domin gano wadanda suka kai harin.

Kwaminishinan ya kuma tabbatar da kai hari kan caji ofis na 'yan sanda dake kusa da wajen amma ya ce babu hasarar rai ko jikkkata sai dai an ƙona motocin yan sanda guda biyu, kuma ba a kama ko daya daga cikin maharan ba.

To sai dai kuma shugaban ƙungiyar ma’aikatan kamfanin na Setraco, Auwal Abubakar Jama’are, yace mutanen bakwai da aka sace sun haɗa da ɗan Italiya, da dan Phillipine, ‘yan Birtaniya biyu, da kuma ‘yan Lebanon uku.

Shi dai kamfanin na Setraco, kamfanin gine-gine ne mai hedikwata a Abujan Nijeriya, dake kuma gudanar da kwangiloli musammn na gina hanyoyin mota a Nijeriya, kuma ma’aikatansa sun hada da ‘yan Nijeriya da ‘yan kasashen waje.

Kawo yanzu kuma babu wani mutum ko kungiya da suka dauki nauyin sace 'yan ƙasashen wajen.

A Nijeriya an sha samun sace-sacen mutane 'yan ƙasashen waje, inda a wasu lokutan akan yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.