Shugaba Jonathan ya bukaci a ceto mutanen da aka sace

Shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya umarci jami'an tsaron kasar da su dauki dukkan matakan da za su kai ga ceto 'yan kasashen wajen nan da ke aiki a wani kamfanin gine-gine da aka kame a garin Jama'are dake jihar Bauchi a arewacin Najeriya.

Shi ma ministan harkokin wajen Labanon Adnan Mansour ya ce suna aiki tare da hukumomin Najeriya domin su ga an sako 'yan kasashen nasu da ake tsare da su.

Kungiyar Jama'atu Ansarul Muslimeena fee Biladissudan ta yi ikirarin cewa ita ce ta kame 'yan kasashen wajen bakwai da suka hada da 'yan Labanan da kasashen turai.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta aike wa manema labarai.

Ansaru ta ce ta kame 'yan kasashen wajen ne, saboda abin da ta kira zargin zaluncin da kasashen Turai ke yi wa Musulunci a Afghanistan da Mali.

Kungiyar ta ce idan kasashen Turai ko Najeriya suka yi yunkurin yin wani abu da ya saba wa sharudanta, to hakan zai kai ga maimaicin abin da ya faru a baya.

Kungiyar ba ta yi karin bayani a kan ko menene sharudanta ba, ko kuma meye ya faru a baya.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin da alama kungiyar na nuni da abin da ya faru a lokacin da Sojojin Najeriya da tallafin Birtaniya suka yi yunkurin ceto wani dan Burtaniya da dan Italiya da aka sace a shekarar 2011.

Amma kuma mutanen biyu suka rasa rayukansu a yunkurin.

An sace ma’aikatan ne dake aiki da kamfanin Setraco mallakar ’yan kasar Lebanon, a garin Jama’are na Jihar Bauchi dake arewa maso gabashin kasar.

Wacece Ansaru

Kungiyar ta jama'atu Ansarul Muslimeena Fi Biladissudan dai ba a santa sosai ba, kamar yadda aka san kungiyar jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram.

A baya dai kungiyar da ake cewa Ansaru a takaice, ta ce ita ta yi garkuwa da wani dan kasar Faransa a watan Disamban da ya gabata.

Sannan ta yi ikirarin kai hari kan shalkwatar rundunar 'yan sanda ta musamman, mai yaki da fashi da makami dake Abuja.

Ta kuma yi ikirarin kai hari a kan sojojin Najeriya dake kan hanyarsu ta zuwa samun horo, domin a tura su aikin kiyaye zaman lafiya a Mali.

A watan Nuwamban da ya gabata ne, Birtaniya ta sanya kungiyar ta Ansaru a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda, inda ta ce ta gano kungiyar na da alaka da kungiyar Alqaida.