Kudadan samar da ruwan sha a Najeria

A Najeriya, a yau aka fara wani taro na musamman da nufin gano ingantattun hanyoyin samar da tsaftataccen ruwan sha ga al'umar kasar.

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ne ya jagorancin taron da kwararru daga ciki da wajen kasar za su yi musayar ra'ayi a kan wasu hanyoyin samun kudade na daban domin inganta ruwan sha.

Rashin tsaftataccen ruwan sha a Najeriya dai wata babbar matsala ce da ta addabi birnin da kauye a kasar, inda jama'a ke ta kokawa akai.