Kotu ta bayar da belin Oscar Pistorius

Oscar Pistorius
Image caption Oscar Pistorius ya ce a bisa kuskure ne ya kashe Reeva Steenkamp

An bayar da belin dan tseren Afrika ta Kudu Oscar Pistorius, wanda ake tuhuma da kisan budurwarsa, bayan wani dogon zaman jin bahasi.

Dan tseren wasan nakasassun ya musanta kisan, yana mai cewa ya harbe Reeva Steenkamp ne bayan da yayi zaton cewa wani ne ya shiga gidansa ba tare da izini ba.

Sharadn belin sun hada da ya rinka mika kansa ga jami'an 'yan sanda sau biyu a kowanne mako.

Zai biya kudin beli dala 113,000 wato miliyan daya na kudin Rand na Afrika ta Kudu, tare da mutanen da za su tsaya masa.

Sannan za a kwace dukkan makaman da ya mallaka tare da hana shi shan giya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Masu gabatar da kara sun nemi kada a bayar da belinsa saboda akwai yiwuwar Mr Pistorius, mai shekaru 26, zai gudu.

Sai dai mai shari'a Desmond Nair ya ce bai gamsu cewa dan wasan zai gudu ba, ko kuma cewa mutum ne mai son tashin hankali.

Karin bayani