An ƙaddamar da sabuwar jam'iyya a Afurka ta kudu

Image caption Mamphela Ramphele 'yar siyasa Afruka ta kudu

Ɗaya daga cikin 'yan fafutukar yaki da wariyar launin fata a Afrika ta Kudu Dr. Mamphela Ramphele, ta kafa sabuwar jam'iyyar siyasa domin ƙalubalantar jam'iyyar ANC mai mulkin ƙasar.

Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya ga bayan yunƙurin da aka yi na cire shi daga shugabancin ANC duk da zargin cin hanci da rashawar, da ƙaruwar rashin daidaito da rashin ayyukan yi tsakanin matasa.

Dr. Ramphele, wacce ke da shekaru 65 a duniya, tsohuwar manajar darakta ce a bakin duniya, kuma farkar dan fafutukar nan da aka yiwa kisan gilla ne Steve Biko, wanda suka haifi ɗa tare.

Haka kuma ta yi aiki tare da Nelson Mandela.