Kamfanin Amurka ya zargi China da kutse ta Intanet

Intanet a China

Wani kamfanin kula da tsaro na harkokin sadarwar internet a Amurka, ya ce wani bangare na rundunar sojin China ne ke da alhakin harin da aka kaiwa na'urorin kwamfyuta na wasu kamfanoni a Amurka.

Kamfanin mai suna Mandiant, ya ce ya bi diddigin harin zuwa wata cibiya a birnin Shanghai, kuma yana da yakinin cewa wata rundunar sojin China mai gudanar da ayyukanta cikin sirri ce ta sace daruruwan bayanai.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China Hong Lei, ya ce rahoton ba shi da wata makama.

Yana cewar satar bayanai a internet matsala ce ta kasa-da-kasa wadda ya kamata a shawo kanta ta hanyar yarda da mutunta juna da kuma hadin kai.

An tsare tawagar BBC da ke bincikar zargin na wani dan lokaci sannan aka kwace hoton bidiyon da suka dauka.

Karin bayani