Gbagbo ya bayyana a gaban ICC

Tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, ya bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague, a fara zaman saurarar tabbatar da tuhumar da zai fuskanta.

Ana zargin Mr Gbagbo da aikata muggan laifukan kan bil'adama bayan zaban shugaban kasar Ivory Coast din da akai a shekara ta 2010 da akai ta takaddama akansa.

Mai shari'a--- Silvia Fernandez De Gurmendi---- dake saurarar karar ta ce wannan shi ne zama na karshe a shari'ar share fagen da zata tantance ko akwai isassun shaidun da za su sa a yiwa Mr Gbagbo shari'a.

Daruruwan magoya bayan tsohon shugaban na Ivory Coast Laurent Gbagbo sun yi dandazo a kofar kotun ta ICC yayin da a waje guda yan sanda ke sanya idanu sosai akan su.

Mutanen dai na cewa sakonnin da suke tafe da su guda biyu ne shugabansu Lauren Gbagbo ba shi da laifi kuma sun zo nan ne domin su nuna masa goyon baya.

Sai dai kuma a cikin kotun a lokacin da tsohon shugaban na Ivory Coast Laurent Gbagbo ya baiyana a gaban mai shari'a, ya zaune tsit ba tare da yin motsi ba yayin da mai gabatar da kara Fatou Bensouda ta ke baiyana zargin da ake masa na jefa kasar cikin rudani domin ci gaba da damfarewa akan karagar mulki bayan da ya sha kaye a zaben 2010.

Mai shekaru 67 da haihuwa Gbagbo shi ne kadai tsohon shugaban kasar da aka gurfanar a gaban kotun wadda kimar da martabarta ke rawa bayan durkushewar wasu shari'u da dama dake gabanta.

Mutane kimanin 3000 ne aka kiyasta cewa sun rasu a rikicn da ya biyo bayan zaben da kuma ya yadu daga babban birnin zuwa wasu sassan kasar har tsawon watanni hudu.

A waje guda lauyoyin dake kare Gbagbo sun zargi kotun da nuna banbanci domin dadadawa abokin hamaiyarsa Alassan Ouattara wanda tsohon ma'aikaci ne na asusun bada lamuni na duniya IMF wanda kuma ya yi alkawarin sake farfado da tattalin arzikin kasar wadda ta kasance kan gaba wajen arzikin Koko a duniya.