ARN ta zargi ONC da nuna musu banbanci

Madugun 'yan adawa na Jamhuriyar Nijar, Alhaji Seyni Omar ya zargi hukumar sadarwa ta kasar, ONC da nuna sakaci wajen tafiyar da aikinta.

Alhaji Seyni Omar ya ce hukumar, tana bari kafofin yada labarai mallakar gwamnati na nuna ma yan adawan wariya da bambanci.

Madugun yan adawan ya ce hukumar sadarwar ba ta sa ido domin tabbatar da cewa dukkan jam'iyun siyasan kasar sun yi amfani da kafofin yada labarai mallakar gwamnati ba tare da wani bambanci ba.

Sai dai hukumar sadarwar ta yi watsi da wannan zargi tana mai cewa ba shi da tushe.