An manna kasidun musanta tsagaita wuta

Shugaban kungiyar Boko Haram, Imam Abubakar Shekau
Image caption Shugaban kungiyar Boko Haram, Imam Abubakar Shekau

Al'ummar Maiduguri a jihar Borno da ke arewacin Najeriya, sun wayi gari da wasu kasidu manne a jikin massallatai da turakun wutar lantarki.

Takardun na dauke da sakon da ke cewa, sun fito ne daga jagoran kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal jihad da aka fi sani Boko Haram, Imam Abubakar Shakau.

Sakon dai ya yi watsi da maganar tsagaita bude wuta, da wani wanda ya ce yana magana da yawun shugaban kungiyar ya yi, a baya-bayan nan.

Wasu al'ummomin birnin sun ce tun a yammacin ranar Talata ne suka samu kasidun da aka rarraba, ko aka lika a unguwanni daban-daban na birnin.

Sai dai kwamishinan yada labarai na jihar Borno, Inuwa Buwala yace bashi da masaniya a kan hakan, amma yana bincike.

Gwamnatin jihar Borno ce ta yi ikirarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da mutumin da ya yi ikirarin magana da yawun shugaban kungiyar ta Boko Haram.

Ita dai kungiyar a yawancin lokuta takan fitar da sanarwa ne ta hanyar sako na Email, ko hira da 'yan jaridu ta waya, ko kuma sakon bidiyo a shafin Youtube na intanet.

Sai dai a lokuta da dama a baya ma, Boko Haram ta fitar da sakonni ta hanyar lillika kasidu a wasu wurare .