Amurka za ta ci gaba da kashe kudaden ta a waje

John Kerry
Image caption Amurka zata ci gaba da kashe kudade a waje

A wani babban jawabi da ya gabatar tun bayan ya hau kan mukaminsa, Sakataren harkokin wajen Amurka, John kerry, ya goyi bayan ci gaba da kashe kudaden da Amurka ke yi kan harkokin kasashen waje a yanzu.

Da yake jawabi a jami'ar Virginia, John Kerry, ya ce amfani da jami'an diplomasiyya wajen sasanta al'amura a yau, ya fi arha a kan tura sojoji gobe wajen murkushe matsalar da ka iya tasowa.

Ya kuma ce bayar da taimako ga kasashen ketare, wani babban zuba jari ne a kimar Amurka a matsayin wata kasa mai karfin fada a ji.

Kerry ya kuma yi gargadin cewa sa'insar da ake ci gaba da samu tsakanin 'yan majalisa game da kasasin kudin kasar, zai sanya a rage tallafin da Amurka ke baiwa kasashen ketare, ya kuma lalata kimarta.

Karin bayani