'Cin hanci na barazana ga harkokin wasanni'

Image caption Shugaban FIFA, Sepp Blatter

Mai rikon mukamin shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Asiya ya ce matsalar cin hanci da rashawa na barazanar watsa harkokin wasanni.

Zhanji Lon na jawabi ne a wajen wani taron kwanaki biyu a kan yin coge a wasa a Kualalumpur.

Ya yi kira da a tashi tsaye wajen ilimantar da 'yan wasa da kuma jami'an wasanni.

Hukumar 'yan sanda ta duniya da kuma hukumar kwallon kafa ta duniya ne suka shirya taron.

A farkon wannan watan wani rahoton hukumar 'yan sandan Turai ya yi zargin cewa wadansu 'yan caca a Singapore suna shirya coge a daruruwan wasannin kwallon kafa a kasashen duniya daban-daban.

Karin bayani