Ambaliya: mutane na komawa gidajensu

Image caption Barnar da ambaliyar ruwa ta yi a Najeriya

A Najeriya, mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu a Najeriya a bara, na ci gaba da komawa gidajen duk da yake hukumomi sun yi gargadi game da hakan.

A cewar mutanen, talauci da rashin sabon mutsuguni ne suka sanya su koma gidajen nasu bayan ruwa ya janye daga gidajen.

Wadansu mutane da suka koma gidajen na su a jihar Kaduna, sun shaidawa BBC cewa ba za su fice daga gidajen ba, sai gwamnati ta samar mu su da sababbin gidaje.

Hukumar bayar da agajin gaggawa, NEMA ta yi kira ga mutanen da su guji komawa gidajen na su saboda hasashen da aka gudanar a bana, ya nuna cewa za a samu ruwan sama mai karfin gaske, wanda zai iya yin mummunar barna.

Karin bayani