Kila-wa-kala game da makomar Faransawa da aka sace

Taswirar Kamaru
Image caption Taswirar Kamaru

Gwamnatocin Faransa da Nijeriya sun musanta wasu rahotanni da ke cewar an gano Faransawar nan bakwai da aka yi awon gaba dasu a arewacin Kamaru.

Tun farko dai, Ministan kula da 'yan mazan jiya na kasar Faransa ya bayayna a gaban majalissar dokokin Faransa cewa an gano Faransawan a wani gari a arewacin Nigeria, amma daga bisani ya janye maganarsa yana mai cewar babu wani tabbasci a kan labarin.

An dai yi ta samu rahotanni masu karo da juna a kan al'amarin, inda wata majiya ta sojojin Kamaru ita ma ta ce an gano Faransawan.

Rahotanni na baya baya na cewa an gano inda ake rike da Faransawar, kuma jami'an tsaro sun kewaye wurin, sai dai babu wata majiyar tsaro da ta tabbatar da gaskiyar hakan ya zuwa yanzu.

Karin bayani