Akalla mutum 12 sun halaka a birnin Hyderabad

Inda bama bamai su ka tashi a Hyderabad
Image caption An bayyana harin a matsayin na ta'addanci

Mutane akalla 12 ne aka kashe a lokacin da wasu tagwayen bama bamai suka tashi a birnin Hyderabad na kudancin India.

'Yan sandan India sun bayyana shi a matsayin wani harin ta'addanci da aka shirya a tsanake.

Bama baman sun tashi ne a cikin wata kasuwa dake cike da mutane da yamma.

Mutane 70 ne su ka samu raunuka sannan akwai shakkun cewar yawan mutanen da suka mutu zai iya karuwa.

Ministan cikin gida ya ce an shedawa jami'an gwamnati game da rahotannin bayanan sirri dake nuni da yiwuwar hare hare a ko'ina cikin kasar.

Karin bayani