Mexico ba ta yi bincike kan mutanen da suka bata ba

Image caption Enrique Pena Nieto

Kungiyar kare hakkin dan adam, Human Rights Watch, ta ce Mexico ta gaza yin bincike don gano dubban mutanen da suka yi batan-dabo karkashin mulkin tsohon shugaba Felipe Calderon.

Kungiyar ta zargi dukkanin jami'an tsaron kasar da hannu wajen bacewar mutanen, tana mai cewa masu safarar miyagun kwayoyi ne ke sanyawa mutane na bacewa.

Wadansu alkaluman gwamnati da aka tseguntawa 'yan jarida a shekarar 2012, sun nuna cewa mutanen da suka bata a kasar sun kai dubu 25, 000.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin shugaba Enrique Pena Nieto ta gaggawa shawo kan matsalar.

Gabanin fitar da rahoton na Human Rights Watch dai, ministan harkokin cikin gida na Mexico, Miguel Angel Osorio, ya yi wata tattaunawa da kungiyar, sannan ya yi alkawarin daukar matakan gaggauwa, wadanda suka hada da samar da hukumar da za ta gano gawawwakin mutanen da suka bata.

Karin bayani